28 Oktoba 2020 - 11:57
Al’ummar Kasar Sudan Sun Bude Fafutuka Gadan-dagan Domin Nuna Adawar Kulla Alakar Da Kasarsu Ta Yi Da HKI

A yau Talata ne dai masu fafutuka a kasar ta Sudan su ka bude gudanar da wasu shirye-shiryen na nuna adawa da alakar kasar tasu da HKI, domin dawo da matsayin kasar na nuna goyon bayan ga kungiyoyin gwagwarmaya a duk inda suke a duniya.

ABNA24 : Wani mai fafutuka a kasar ta Sudan, Usman Kabbashi ne ya sanar da kafa wata cibiya ta kasa ta fada da mu’amala kowace iri da HKI.

Kabbashi ya kara da cewa wasu tsirarun mutane masu alaka da ‘yan mulkin mallaka, sun yi garkuwa da juyin juya halin da al’ummar Sudan su ka yi.

Har ila yau Kabbashi ya ce; Khartum za ta ci gaba da zama birnin ya ki amincewa da yin hulda, ko tattaunawa balle kulla alaka da ‘yan sahayoniya.

A ranar 25 ga watan nan na Oktoba ne dai Sudan ta sanar da shiga cikin sahun kasashen larabawa masu kulla alaka da HKI.

342/